Mun yi amfani da makamin Sejil karon farko kan Isra'ila - IGRC
Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta ce ta yi amfani da wasu nau'in makamai masu linzami kan Isra'ila karon farko tun bayan fara wannan yaƙin.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar ya ce sun yi amfani da makaman ''Khorramshahr, mai nauyin gaske, wanda ke da kawuna biyu da makaman Khyber-Shakan da Qadr da Emad, waɗanda duka masu linzami ne.
A cewar rundunar makamin Sejil, matsakaicin makamai ne da ake harbawa dada kan doron ƙasa, wanda ke amfani da man fetur, kuma zai iya tafiyar tazarar tsakanin Natanz zuwa Tel Aviv a cikin minti bakwai.
A dai dai lokacin da rundunar ke fitar da wannan sanarwa, sojojin Isra'ila sun bayyana gano makaman linzami na Iran da suka nufi ƙasar.
Hare-haren na zuwa ne ƙasa da sa'a biyu bayan bayar da rahoton wasu hare-haren.