Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2026 da yawansa ya kai naira tiriliyan 68.32.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce cikin wannan adadi za a ware naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashi.

Kasafin ya kuma ware naira tiriliyan 15.4 domin ayyukan gudanarwar yau da kullum, yayin da aka ware naira tiriliyan 32.2 don gudanar manyan ayyuka.

"Yayin da kusan rabin kasafin zai tafi a manyan ayyuka, hakan na nuna burin gwamnati na ci gaba da ayyukan daidaita tattalin arziki ta hanyar bunƙasa ɓangaren tsaro da samar da ayyukan more rayuwa da ci gaban kowane fanni'', in ji sanarwar.

Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci hukumomin gwamnati su tabbatar da bin ƙa'ida da yin komai a bayyane da amfani da kuɗaɗen da aka ware musu ta hanyoyin da suka dace.

Tinubu ya yaba wa majalisa kan kasafin

Shugaban na Najeriya ya yaba wa majalisar dokokin ƙasar kan abin da ya kira tsafe kasafin tare da bayar da haɗin kai da nuna kishin ƙasa wajen amincewa da kasafin kuɗin.

Haka kuma shugaban ƙasar, ya jaddada muhimmancin haɗin kai da aiki tare tsakanin ɓangaren majalisar da na zartarwa wajen ciyar da ƙasar gaba.

Ana sa ran ciyo bashin dala biliyan 21 domin cike giɓin kasafin kuɗin.

Tinubu ya ɗage aiwatar da kasafin 2025

Haka kuma sanarwar ta ce shugaban na Najeriya ya ɗage fara aiwatar kasafin kuɗin ƙasar na 2025 zuwa 30 ga watan Yunin 2026.

Tun da farko an tsara fara aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 ɗin a ranar 31 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

A watan Dismaban 2025 Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar kasafin 2026 na naira tiriliyan 58.47domin neman amincewarta, wanda a lokacin adadin kuɗin da aka gabatar shi ne.

Daga baya kuma ya ƙara naira tiriliyan 9 a kasafin.

Tun da farko an tsara kasafin a kan hasashen farahin gangar ɗanyen man fetur a kan dala 64.85.

To amma yanzu da farashin an fetur ya zarta dala 100 sakamakon yaƙin Iran, masana tattalin arziki na hasashen samun raguwar giɓin kasafin.