Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Adam A. Zango ba shi ne Bahaushen da ya fi shahara ba - Sheme
Shin wane ne Bahaushen da ya fi kowa shahara a duniya?
Wadanne ma'aunai ake amfani da su don tantance mutumin da ya fi shahara a tsakanin Hausawan duniya?
Wadannan na daga cikin tambayoyin da suka biyo bayan ikirarin fittacen tauraron nan na masana'antar Kannywood Adam A. Zango, kuma wannan batu dai ya haddasa muhawara a shafukan sada zumunta.
BBC ta tambayi fitaccen marubucin nan kuma mai sharhin fina-finan Hausa, Ibrahim Sheme don jin sahihancin ikirarin na Adam A. Zango.